Kotu ta samu jarumin Hotel Rwanda Rusesabagina da laifin ta'addancin
Wata kotu a Rwanda ta samu Paul Rusesabagina, da yayi fitce a fim din ‘Hotel Rwanda’ da kamfanin shirya fina finan Amurka a shekarar 2004 da laifin ta’addanci.
Wallafawa ranar:
Da take sanar da hukuncin Alkali Beatrice Mukamurenzi tace ta samu mutanen 20 dake gabanta ci harda Rusesa-bagina da laifin kasancewa cikin kungiyar ta’addanci na MRCD-FLN, da suka rika kaiwa mutane hare-hare gidajensu, ko ma tare su cikin motocin su.
Wannan shari’ar dai ta yi kaurin suna tun bayan da aka kama Rusesabagina, mai shekara 67, a bara lokacin ya isar Rwanda daga Dubai, yana mai bayyana matakin a matsayin garkuwa da shi hukumomin Rwanda suka yi.
Rusesabagina wanda yayi fitce a fim din Hotel Rwanda da Hollywood na Amuka ta shirya game da kisan kiyashin shekarar 1994, ya dade yana sukar shugaban kasa Paul Kagame, wanda yake bayyana shi a matsayin dan kama karya, kafin a kama shi a watan Agustan bara.
Masu gabatar da kara sun bukaci kotu ta yankewa Rusasebagina hukuncin daurin rai-da-rai, a shari’ar da ta gamu da suka daga ciki da wajen Rwanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu