Shugaba Paul Kagame na ziyara Mozambique
Shugaba Paul Kagame na Rwanda a yau Juma’a ya fara ziyarar kwanaki biyu a Mozambique don karawa Dakarun kasarsa karfin guiwa a kokarin taimakawa Mozambique yakar ‘yan ta’adda da suke barna a kasar.
Wallafawa ranar:
A watan 7 da ya gabata ne dai ta aike da Dakarunta dubu daya, Mozambique karkashin wani kokarin kasashen yankin don yakar masu jihadi da karfin tsiya da suka dade suna cin karensu ba babbaka a yankin Cabo Delgado mai arzikin skar gas dake Mozambique.
A yau Juma’a Paul Kagame ya sauka a birnin Penba, kuma cikin abubuwanda zai yi cikin kwanakin biyu da zai yi a kasar zai gana da sojojin kasarsa da ‘yan sanda dake aikin daukin,
Dakarun kasashen waje dai sun taimakawa Mozambique farfadowa daga halin kunci da aka shiga a kasar saboda ayyukan masu jihadin.Kungiyar kasashen yankin su 16 sun yi alkawarin aikewa da gudunmawar Dakaru 1,500.
A yanzu haka kuma Kungiyar Tarayar Turai ta fito da tsarin aikewa da dakarun musamman da za su horasda sojan na Mozambique dabarun yaki
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu