Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Faransa ta musanta yunkurin juya baya ga Mali kan sha'anin tsaro

Faransa ta sake yin watsi da zarge-zargen cewa ta juya baya ga Mali ta hanyar janye dakarunta duk da halin da kasar ta yammacin Afrika ke ciki a yanzu sakamakon tsanantar ayyukan ta’addanci.

Ministar tsaron Faransa Minister Florence Parly.
Ministar tsaron Faransa Minister Florence Parly. Paul Lorgerie/Reuters
Talla

Ma’aikatar tsaron Faransa da ke musanta zargin ta hanyar kakakinta Anne-Claire Legendre ta ce sauya fasali ko kuma salon tunkarar matsalolin tsaron da yankin Sahel ke fuskanta da kasar ta yi baya nufin ta janye daga Mali.

Karuwar zarge-zargen Faransa na kokarin janyewa daga Malin na zuwa ne bayan da Firaministan kasar ta Sahel Choguel Kokalla Maiga ke cewa uwar goyon na su na kokarin janyewa daga kasar daidai lokacin da rikici ke tsananta ta hanyar rage yawan sojojinta da ke taimakawa a yaki da ta’addanci cikin kasar.

A jawabinsa gaban wani bangare na babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya Maiga ya ce abin takaici ne yadda Faransar ke ci gaba da janye dakarunta daga Malin.

Sai dai Anne-Claire da ta ke kare kasar tata, ta nanata cewa Faransar ba ta da shirin janyewa daga Mali, maimakon haka ta na son karfafa yakin da ta ke da ‘yan ta’adda a yankin na Sahel baki daya.

Ko a makon da ya gabata, ministar tsaron faransar, Florence Parly ta musanta cewa kasar na kokarin janyewa daga Malin dungurum tana mai cewa ko kadan kasar ba ta da shirin juya baya ga Malin.

A watan Yunin da ya gabata ne Faransar ta fara rage yawan dakarunta da ke sansanin Kidal da Tumbuctu da kuma Tessalit yayinda ta bayyana shirin rage dakarun a yankin na Sahel daga 5000 zuwa 2500 nan da shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.