Isa ga babban shafi
Rwanda

Hukumomin Rwanda sun kama mutane 13 da ke shirya harin ta'addanci a Kigali

‘Yan sandan Rwanda sun ce sun kama wasu mutane 13 da suke zargin su da shirya hare haren ta’addanci a babban birnin kasar Kigali, kuma sun gabatar da su ga manema labarai.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame. REUTERS - JEAN BIZIMANA
Talla

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar ta ce an kama wadanda ake zargin ne da kayayyakin hada bama bamai da suka hada da wayoyi, kusoshi da wayar hannu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce binciken ta ya nuna mata cewa wadanda ake zargin na da alaka da da kungiyr ‘yan tawaye na ADF da ke aikata ayyukan ta’addanci a makwafciyarta, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Ana zargin kungiyar ADF, wadda ta samo asali daga kasar Uganda da kisan dubban fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimoikaradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.