Isa ga babban shafi
Afrika-Faransa

Macron zai karbi bakoncin taron matasan nahiyar Afrika

Shugaba Emmanuel Macron na shirin karbar bakoncin taron matasan kasashen Nahiyar Afirka wanda zai faro a Juma'a mai zuwa, taron da ke da nufin mayar da hankali kan hulda ta kai tsaye tsakanin kasar ta Turai da matasan nahiyar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AP - Gonzalo Fuentes
Talla

Maimakon sauran shuwagabannin kasashe, Macron ya gayyaci daruruwan matasa da suka kunshi 'yan kasuwa da masu fasaha da kwararru kan harkokin wasanni zuwa kudancin Montpellier.

Sanarwar fadar Elysee game da taron ta ce manufarsa shi ne ganawa tare da tattaunawa kan kalubalen matasan nahiyar ta Afrika baya ga lalubo hanyoyin magance matsalolin da su ka addabesu.

Ganawar tsakanin Macron da matasan na Afrika na zuwa a wani yanayi mai cike da sarkakiya bayan jerin takaddama tsakanin kasar da 'ya'yanta da ta yiwa mulkin mallaka a Afrika baya ga yunkurinta na fara hana biza ga kasashen Algeria, Morocco da Tunisia.

Bayan tsanantar tsamin alakar tsakanin Faransar da diyan goyonta, tuni Algeria ta kora mata jakadanta gida bayan caccakar da Macron ya yiwa kasar na cewa ta na amfani da tsarin mulkin Soja, a bangare guda kuma rikici ke ci gaba da tsananta tsakanin Faransar da Mali.

Kimanin mahalarta dubu 3 ciki har da matasa sama da 1,000 ake sa ran gani a Montpellier don tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da al'adu da kuma siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.