Isa ga babban shafi
Burkina Faso-Sankara

Ana sa ran fara shari'ar kisan Thomas Sankara

Ana saran fara shari’ar kashe tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara a kotun soji dake Ouagadogou, inda ake saran mutane 14 su gurfana a gaban shari’a.

Thomas Sankara, tsohon shugaban Burkina Faso da aka kashe a 198
Thomas Sankara, tsohon shugaban Burkina Faso da aka kashe a 198 DOMINIQUE FAGET AFP/File
Talla

Cikin mutanen da ake tuhuma da kashe tsohon shugaban kasar shekaru 14 da suka gabata, harda wanda ya gaje shi, kuma aminin sa, Blaise Compaore tare da wasu mutane 13.

Lauyoyin Compaore sun ce ba zai kaurace wa zaman kotun saboda zargin cewa ba za a mai adalci ba.

Blaise Campore ya mulki kasar tsawon shekaru 27 kafin a hambarar da shi ta wajen wata zanga zanga a shekarar 2014, inda ya arce zuwa makwfaciyar kasarsa, Ivory Coast, wadda ta ba shi takardar zama dan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.