Isa ga babban shafi
Corona-Kenya

Kenya ta janye dokar hana zirga-zirga saboda corona bayan kusan watanni 20

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da cire dokar takaita zirga zirgar da aka kafa a watan Maris din shekarar da ta gabata, domin yaki da annobar korona, cutar da ke ci gaba da kisan jama'a a sassan Duniya.

Shugaba Uhurru Kenyatta na Kenya.
Shugaba Uhurru Kenyatta na Kenya. AP - Gonzalo Fuentes
Talla

Alkaluma sun nuna yadda annobar ta kashe mutane dubu 5 da dari 2 da 33 a kasar daga cikin mutane dubu 252 da 199 da suka harbu tun bayan bullarta, dai dai lokacin da kashi 5 na jama'ar kasar suka karbi allurar rigakafi.

Shugaba Kenyatta ya sanar da wannan mataki ne lokacin da ya ke jawabi a ranar karrama wadanda suka yiwa kasar yakin neman yancin kai, inda ya ke godewa al'umma kan bin dokar da suka yi a kokarin yaki da cutar.

Shugaba Kenyatta ya ci gaba da cewa, bisa nauyin da aka dora masa na matsayin shugaban kasa, yana mai bada umarnin cewa dokar hana fita daga yamma zuwa wayewar garin da ake amfani da ita daga ranar 27 ga watan Maris din 2020 ta kawo karshe.

Acewar Kenyatta matakin janye dokar zai fara aiki nan ta ke ba tare da bata lokaci ba, don baiwa jama'a 'yancin yin walwala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.