Isa ga babban shafi
Sudan

Masu zanga-zangar Sudan sun yi tsayuwar gwamen Jaki kan adawa da juyin mulki

Al’ummar Sudan sun kwarara kan tituna cikin zanga-zangar nuna adawa da juyin mulki da sojoji suka sake yi a ranar Litinin, abinda ya kawo karshen gwamnatin hadakar kasar karkashin jagorancin Firaminista Abdallah Hamdok.

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a kasar Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a kasar Sudan. - AFP
Talla

Tuni dai manyan kasashe da kungiyoyin duniya suka yi tir da wannan juyin mulkin da suka ce cikas ne ga ci gaban dimokradiyya da kuma koma baya ga kasashen Afirka.

Ana sa ran kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi wani taron gaggawa kan batun.

Tuni dai wasu jakadun kasashen Turai 3 suka fice daga Sudan, domin nuna fushin kasashen duniya game da juyin mulkin da aka yi a kasar, da kuma ayyana ofisoshinsu a matsayin na mutanen Sudan.

Masu zanga-zangar adawa da sake juyin mulkin da sojoji suka yi a Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da sake juyin mulkin da sojoji suka yi a Sudan. AFP - -

Jakadun kasashen da suka bar Sudan din sun hada da na Faransa, Belgium da Switzerland, wadanda suka ce, suna tare da jama’ar Sudan dari bisa dari, kuma basa goyon bayan juyin mulki ta kowacce fuska.

A iya cewa jama’ar Sudan basu gamsu da juyin mulkin ba, la’akari da yadda tun a ranar Litinin suka fara zanga-zangar da ka iya juyewa zuwa bore don adawa da hambarar da gwamnatin Abdallah Hamdok tare da tsare shi, duk da barazanar da sojoji suka yi, bayan da suka bude wutar da ta hallaka mutane uku da raunata kusan 100.

Tun shekarar 2019, Sudan ke karkashin tsarin gwamnatin hadaka, tsakanin shugaba Abdelfatah, Al-Burhan da kuma Firaminista Abdallah Hamdok, wanda kuma tun wancan lokaci kasar ke cikin tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.