Isa ga babban shafi
Senegal-Adabi

Matashin Senegal ya lashe kyautar adabin Faransanci

Wani matashi dan kasar Senegal mai suna Mohamed Mbougar Sarr, ya lashe gasar rubuce-rubuce da addabin harshen faransanci mai girma  da ake kira Concourt, bayan da kwamitin alkalancin gasar ya yi bita dangane da abubuwan da ke kunshe a wani littafen da ya rubuta mai suna "La plus secrète mémoire des hommes’’

Mohamed Mbougar Sarr da ya lashe kyautar adabin Faransanci.
Mohamed Mbougar Sarr da ya lashe kyautar adabin Faransanci. Bertrand Guay AFP
Talla

Bayan sanar da shi a matsayin zakaran gasar ta 2021, Mohamed Mbougar Sarr, ya bayyana farin cikinsa, inda ya ke cewa,

Wannan tukuici muhimmin sako ne daga hukumar raya harshen Faransancin  zuwa ga mutane da dama, da farko zuwa ga marubuta a cikin harshen Faransanci,

 

"Abu na biyu ya kamata a sani cewa wannan tukuici ana bayar da shi ne domin cancanta, saboda haka ba wai an ba ni wannan tukuici ne domin na fito daga nahiyar Afirka ba, sai dai saboda muhimmancin rubutun da ke kunshe a wannan littafe." inji Sarr.

Matashin marubucin ya kara da cewa, babu siyasa wajen bayar da wannan tukuici,  yayin da ya mika godiya ga kwamitin alkalanci na wannan gasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.