Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta fara bincikar zargin da ake yi wa sojojinta na cin zarafin mutane

Rundunar sojin Mali ta sanar da fara gudanar da bincike akan zarge zargen cin zarafin Bil Adama da ake yi wa dakarun kasar yayin yaki da Yan ta’adda.

Sojojin Mali yayin sintirin hadin gwiwa da sojojin Faransa a kauyen Bintagoungou mai nisan kilomita 80 daga Timbuktu a shekarar 2015.
Sojojin Mali yayin sintirin hadin gwiwa da sojojin Faransa a kauyen Bintagoungou mai nisan kilomita 80 daga Timbuktu a shekarar 2015. AFP
Talla

Mai Magana da yawun sojin Kanar Issa Ousmane Coulibaly ya ce sun fara gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin wanda yace yana bata sunan sojin.

Masu fafutukar kare hakkin sun dade suna zargin sojojin Mali da aikata laifukan cin zarafin dan adam, da suka hada da kisan gilla, azabtarwa da kuma batar da mutane.

A cikin watan Afrilu, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta dora alhakin kisan gillar da aka yi wa akalla mutane 34 tare da bacewar wasu 16 akan sojojin Mali yayin gudanar da ayyukansu a tsakiyar kasar a tsakanin Oktoban shekarar 2020 zuwa Maris da ya gabata.

A gefe guda kuma rahoton da aka fitar a shekarar da ta gabata daga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, ya zargi sojojin Mali da aiwatar da hukuncin kisa 101 tsakanin watan Janairu zuwa Maris din shekarar ta 2020.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a bara kuwa ya gano shaidun dake nuna cewa jami'an tsaron Mali da masu ikirarin jihadi dukkaninsu sun aikata laifukan yaki.

Mali dai ta dade tana fafutukar kawo karshen kazamin tada kayar bayan da mayaka masu ikirarin jihadi ke yi tun shekarar 2012, kuma tun daga wannan lokaci ya bazu zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.