Isa ga babban shafi
Congo-ADF

Sojin Jamhuriyar Congo sun kwace yankin da 'yan tawayen M23 suka mamaye

Jami’an Sojin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun sanar da sake kwace yankin da ya kubce daga hannunsu yayin farmakin ‘yan tawaye a karshen makon nan wanda kuma ya hallaka dakaru da tarin fararen hula a gabashin kasar.

Dakarun Sojin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Dakarun Sojin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. ALEXIS HUGUET AFP
Talla

Ma’aikatar tsaron kasar ta zargi mayakan ‘yan tawayen M23 da kaddamar da farmakin kan sansanin sojinta da ke yankin Rutshuru a gabashin kasar.  

Kakakin Sojin kasar Janar Sylvain Ekenge ya ce dakarunsu yanzu haka sun bi sahun mayakan ‘yan tawayen inda suke ci gaba da gwabza yaki don fatattakarsu a kokarin murkushe barazanarsu.

Ko a jiya talata, hukumar kula da 'yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 11 suka tsallaka Uganda daga gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo don gujewa rikicin da yankin ke ci gaba da fuskanta.

Kakakin hukumar Shabia Mantoo ta ce galibin wadanda ke cikin ‘yan gudun hijrar mata ne da kananan yara bayan tsanantar arangama tsakanin dakarun Sojin kasar da kungiyar ‘yan bindigar arewacin Kivu.

Acewar hukumar yanzu haka Uganda na kokarin zama kasa mafi dauke da ‘yan gudun hijira a Afrika bayan wasu masu neman mafaka dubu 8 da suka isa yankin Bunagana da kuma wasu dubu 3 a Kibawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.