Isa ga babban shafi
AFIRKA-MATA

An bude taron kula da 'ya mace na kungiyar AU a Nijar

Yau aka bude taron kula yara mata na kasashen Afirka karo na 3 a birnin Yammai dake Jamhuriyar Nijar, wanda zai yi nazari akan matsalolin dake yiwa yara mata illa wajen cimma burin rayuwar su da zummar samo maslaha.

Shugaba Bazoum Mohammed tare da wakilan dake halartar taron 'ya mace a Nijar
Shugaba Bazoum Mohammed tare da wakilan dake halartar taron 'ya mace a Nijar © Niger Presidency
Talla

Taron na kwanaki biyu wanda shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bude, ya janyo masana da mata daga kasashen Afirka da dama.

Wannan dai shine karo na 3 da kungiyar kasashen Afirka ke gudanar da irin wannan taro wanda ke janyo kwararru akan kare hakkokin yara mata da kuma mata, tare da samun halartar ‘yam mata daga kasashen Afirka sama da 50 domin tafka mahawara da kuma kulla yarjejeniya.

Wakilan dake halartar taron kungiyar kasashen Afirka ta AU akan 'ya mace dake gudana a Nijar
Wakilan dake halartar taron kungiyar kasashen Afirka ta AU akan 'ya mace dake gudana a Nijar © Niger Presidency

Yayin jawabin bude taron, kwamishiniyar kula da jin dadin jama’a ta kungiyar kasashen Afirka wato AU, Amira ElFadil ta jinjinawa Nijar akan rawar da take takawa wajen kula da mata da kuma ’yam mata musamman abinda ya shafi basu ilimi, kula da rayuwar su da kuma kare hakkokin su.

Wasu ’yam mata daga kasashen Somalia da Zambia da kuma Jamhuriyar Nijar da suka yiwa taron jawabi, sun bayyana irin damuwar da suke fuskanta da kuma ‘yancin da suke da bukata na tafiyar da rayuwar su yadda suke so, musamman abinda ya shafi samun ilimi da kuma kwarewa a fannoni daban daban na rayuwa kana da yin aure a lokacin da suke bukata.

Kungiyar mawakan Sogha lokacin da suke bada tasu gudumawa wajen taron
Kungiyar mawakan Sogha lokacin da suke bada tasu gudumawa wajen taron © Niger Presidency

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya jaddada matsayin gwamnatin sa na kare ‘ya mace da kuma bata ilimi kamar kowanne ‘dan kasa, yayin da yayi karin haske akan matakai daban daban da gwamnatin sa ke dauka wajen ganin ’yam mata sun samu kula ta musamman da zasu cimma burin rayuwar su ba tare da sanya musu wani shinge ba.

Bazoum ya bayyana irin matakan da kasar ke dauka na dakile yiwa ‘yam matan aure da wuri da kuma haramta kaciyar da ake yiwa wasu daga cikin su wanda ke musu matukar illa.

Ana saran kammala taron na kwanaki 2 a ranar alhamis mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.