Isa ga babban shafi
Togo

Dokar Hana Ganin Fursunoni Na Aiki A Gidajen Yari Dake Kasar Togo

Hukumomi a kasar Togo sun haramtawa dangi da ‘yan uwan fursunoni dake gidajen yari a fadin kasar kai duk wata ziyara don saduwa da fursunoni dake zaman kaso.

Shugaba Faure Gnassingbé, na Togo.
Shugaba Faure Gnassingbé, na Togo. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Watanni 18 kenan da aka kafa wannan doka don a yaki cutar Corona daga kama shiga gidajen yari.

Mutane da yawa daga cikin dangi da ‘yan uwan fursunoni dake gidan kaso sun koka matuka saboda wannan mataki dake hana su ganin mutanensu.

Ministan Sharia na kasar Pius Agbetomey tun a bara ya sanar da cewa an hana kai ziyara gidajen yari dake fadin kasar har sai illamasha’a saboda annobar cutar Corona.

Yanzu haka akwai mutane 26,167 da aka gano sun harbu da kwayar cutar Corona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.