Isa ga babban shafi
ZANGA-ZANGAR-SUDAN

Jami'an tsaro sun harbe mutane 15 a Sudan

Jami’an Tsaro a kasar Sudan sun harbe mutane 15 har lahira daga cikin masu zanga zangar adawa da juyin mulkin da soji suka yi a watan jiya, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban daban.

Shugaban juyin mulkin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan
Shugaban juyin mulkin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ASHRAF SHAZLY AFP/File
Talla

Adadin wadanda aka kashe a birnin Khartoum ya tashi zuwa 39 tun bayan juyin mulkin da sojoji suka sake yi a ranar 25 ga watan Oktoba kamar yadda kungiyar likitocin kasar ta sanar.

Kungiyar kwararrun ma’akatan kasar tace kisan da aka yiwa masu zanga zangar ya dada karfafa su, saboda haka ba zasu bada kofar tattaunawa ko hadin kai ko kuma watsi da bukatun su ba wajen ganin sojojin sun bar karagar mulki.

Masu zanga zanga a Sudan
Masu zanga zanga a Sudan AP - Marwan Ali

Masu zanga zangar sun mamaye titunan birnin Khartoum duk da katse layukan sadarwa da kafofin intanet da sojojin suka yi.

Masu zanga zangar wadanda akasarin su matasa ne maza da mata, sun ce bukatar su itace mulkin farar hula, yayin da suke kalamun nuna rashin amincewa da jagorancin Janar Abdel Fatah al-Burhan.

Hotunan bidiyo sun nuna wasu masu zanga zangar na jifar jami’an tsaro da duwatsu, yayin da su kuma suke mayar da martini da hayaki mai sa hawaye da kuma harsasai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.