'Yan Sandan Uganda sun hallaka mayakan ISWAP
Rundunar Yan sandan Uganda ta harbe wasu mutane 5 har lahira da ake zargi da ayyukan ta’addanci, yayin da ta kama wasu 21 bayan kazamin harin kunar bakin waken da aka kai Kampala wanda kungiyar ISWAP ta dauki alhaki.
Wallafawa ranar:
Kunna - 00:52
Daga cikin mutanen da aka kashe harda Sheikh Sharifu dake daukar mutanen dake shiga cikin kungiyar ADF kamar yadda kakakin Yan Sandan Kampala Fred Enanga ya shaidawa manema labarai.
Sheikh Muhammed Sherifu na daya daga cikin shugabannin dake da hannu dumu dumu wajen daukar mutane zuwa cikin kungiyar ADF. Kuma yana daya daga cikin masu sake dawo da aikan ta’addancin kungiyar ADF a yankin Kampala. Abin takaici ne yadda ya mutu ta wannan hanya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu