Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Cote d'Ivoire na bincike kan zargin fyade da ake yi wa jami'an tsaron ta

Kasar Ivory Coast na gudanar da bincike kan ikirarin jami'an tsaron kasar sun yi wa mata biyar fyade a lokacin da suke gudanar da aikin hakar zinare ba bisa ka'ida ba a yankin arewa maso gabashin kasar, in ji wani dan majalisa da wata majiya da ke bin lamarin.

Jami'an tsaron Ivory Coast 17/06/21.
Jami'an tsaron Ivory Coast 17/06/21. REUTERS - LUC GNAGO
Talla

Noufe Sansan, dan majalisar dokokin kasar ya ce an kai harin ne a farkon makon nan a kauyen Lagbo da ke mazabarsa kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Daga cikin mata biyar da aka bayar da rahoton cewa an ci zarafinsu, “uku sun amince su shigar da kara a hukumance,” Amma "su biyu sun gudu daga ƙauyen saboda kunya."

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar da rahotannin sannan ta ce hukumomi sun kaddamar da bincike mai zurfi kan lamarin.

Fara bincike

A ranar Juma'a ce mai gabatar da kara a birnin Bouna da ke kusa da garin ya je kauyen domin gudanar da bincike, kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana.

Rundunar yaki da hakar zinare

A cikin watan Yuni ne kasar Ivory Coast ta kafa wata runduna ta musamman domin dakile aikin hakar zinare ba bisa ka'ida ba a kasar, wanda ya kunshi jandarmomi 460 da jami'ai 100 na sashen ruwa da gandun daji.

Ya zuwa yanzu sun lalata haramtattun wurare 69 tare da kama mutane 261, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.