Isa ga babban shafi
Somalia

Dan kunar bakin wake ya kashe shahararren dan jarida a Somalia

Wani dan kunar bakin wake ya kashe fitaccen dan jaridar kasar Somalia da ya shahara wajn caccakar kungiyar al-Shabab a yayin da yake fita daga wani gidan cin abinci a Mogadisahu, babban birnin kasar.

Taswirar Somalia dake nuna babban birnin kasar, Mogadishu.
Taswirar Somalia dake nuna babban birnin kasar, Mogadishu. AFP
Talla

Al-Shabab  ta dau alhakin harin, wanda ya kashe daraktan gidan Radion Mogadishu, Abdiaziz Mohamud Guled, wanda ake wa inkiya da Abdiaziz Afrika.

Harin ya raunata mutane da dama, ciki har da daraktan gidan talabijin Somalia da wani direba.

A watan sanarwa, mataimakin ministan yada labaran Somalia, Abdirahman Yusuf Omar ya ce kasar ta yi asarar jajirtaccen namiji.

Abdiaziz ya yi fice ne saboda wani shirinsa da yake ganawa da ‘yan kungiyar al-Shabab da jami’an tsaron Somalia ke tsare da su, shirin da ya samu dimbim mabiya a ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.