Isa ga babban shafi
Sudan

An saki dimbin fararen hular da aka kama a Sudan

Mahukunta a Sudan sun sallami fararen hula da dama da aka kama lokacin zanga-zangar da ta biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa firamista Abdallah Hamdok. Sakin mutanen daga inda ake tsare da su na zuwa ne kwana daya bayan da sojoji suka sake dawo da Hamdok a kan mukaminsa.

Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da mulkin soji
Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da mulkin soji © AP Photo/Marwan Ali
Talla

Matakin sallamar illahirin mutanen da aka kama lokacin zanga-zangar da ta barke biyo bayan wannan juyin mulki, na daya daga cikin abubuwan da ke kunshe a yarjejeniyar da aka cimma tsakanin janar Abdel Fatah Al-Burhan da kuma Abdallah Hamdok.

Jagoran jam’iyyar Sudan Congress Party Omar al-Degeir, na daya daga cikin mutanen da aka sallama a cikin daren jiya bayan kama shi a ranar 25 ga watan Okotban da ya gabata lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin firaminista Hamdok.

Wasu daga cikin mutanen da aka sallama har da magoya bayan jam’iyyar Umma, daya daga cikin kungiyoyi da kuma jam’iyyun da suka jagoranci zanga-zangar adawa da mulkin soji a Sudan.

Bayanai dai na nuni da cewa daruruwan mutane ne aka kama bayan barkewar wannan tarzoma, yayin da akalla wasu mutanen 41 suka rasa rayukansu mafi yawansu a birnin Khartum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.