Isa ga babban shafi
TARON-ZAMAN LAFIYA

Buhari ya sake bayyana damuwa akan rashin zaman lafiya a Afirka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake bayyana damuwa akan yadda zaman lafiya ya gagari kasashen Afirka da dama, matsalar da yace tana yiwa nahiyar tarnaki wajen ci gaban ta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen taron matan shugabannin Afirka karo na 9 a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen taron matan shugabannin Afirka karo na 9 a Abuja © Nigeria presidency
Talla

Buhari wanda ke bude taron kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka karo na 9 a Abuja, yace ayyukan ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga sun ci gaba da haifar da matsalolin dake raba mutane da muhallan su da kuma sake jefa su cikin kangin talauci.

Shugaban yace babu tantama mata da yara ne suka fi shan radadin illar dake tasowa daga matsalar rashin zaman lafiya, saboda haka ya bukaci matan shugabannin Afirka da su taimaka wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Shugaba Muhammadu Buhari yana bude taron matan shugabannin Afirka
Shugaba Muhammadu Buhari yana bude taron matan shugabannin Afirka © Nigeria presidency

Buhari ya bayyana farin cikin sa da yadda taron matan shugabannin ke aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma hadin kai ta hanyoyi daban daban a kasashen su, yayin da ya bukaci taimaka musu wajen cimma muradun su na tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Daga karshe Buhari ya yabawa uwargidan sa Aisha akan kokarin da tayi wajen mallakar filin da za’a gina sakatariyar kungiyar a Abuja, yayin da ya bayyana fatar ganin anyi amfani da ita wajen samarwa matasan ayyukan da zasu dogara da kan su.

Buhari da uwargidan sa Aisha da wasu daga cikin matan shugabannin Afirka
Buhari da uwargidan sa Aisha da wasu daga cikin matan shugabannin Afirka © Nigeria presidency

Matan shugabannin sun zabi Aisha Buhari a matsayin sabuwar shugabar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.