Isa ga babban shafi
Guinea

Likitocin Guinea sun yi wa matashiya fyade har lahira

Al’ummar Guinea sun gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu kan mutuwar wata matashiya da likitocin kasar suka yi mata fyade a cikin asibiti.

Fyade na cikin manyan abubuwan da ke cutar da rayuwar mata
Fyade na cikin manyan abubuwan da ke cutar da rayuwar mata © firstpost
Talla

Tuni dai hukumomin Guinea suka cafke likitoci uku da ake zargi da yi wa matashiyar mai suna M’Mah Sylla fyade  bayan ta rasa ranta a birnin Tunis na Tunisa, inda ake yi mata magani.

Sylla ta mutu ne a ranar Asabar da ta  gabata kamar yadda gwamnatin Guinea Conakry ta sanar a ranar Lahadi.

Jaridun Guinea sun rawaito cewa, matashiyar ta ziyarci asibitin ne a cikin watan Agusta, amma ba a tantance ainihin musabbabin zuwanta asibinta ba duk da dai wasu na ganin , ta je ne don duba lafiyarta.

Hukumomin Tunisia ne dai suka dauki nauyin yi wa budurwar aiki bayan sun dauke ta daga Guinea a cikin watan Oktoban da ya gabata.

Yanzu haka ana zargin wadannan likitoci da aikata  laifuka da dama da suka hada da fyaden da zubar da ciki da dirka wa marigayiyar miyagun kwayoyi kamar yadda masu shigar da kara na gwamnati suka bayyana.

Tuni daya daga cikin likitocin da ake zargi da aika-aikar ya tsere, kuma a halin yanzu ana neman sa ruwa a jallo.

Mutanen Guinea na amfani da kafofin sada zumunta wajen yayata kiraye-kirayen ganin a yi wa marigayirar adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.