Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Mutane da dama sun jikkata a zanga-zangar adawa da gwamnatin Burkina Faso

Mutane da dama sun jikkata a Burkina Faso cikin su harda karamin yaro da 'Yan Jarida guda biyu, sakamakon harba hayaki mai sa hawayen da Yan Sanda suka yi akan masu zanga zangar adawa da gwamnati saboda yadda Yan ta’adda ke kai hare hare a cikin kasar.

Masu zanga-zanga yayin arrangama da jami'an tsaron Burkina Faso a birnin Ouagadougou, ranar 27 ga watan Nuwamba, 2021.
Masu zanga-zanga yayin arrangama da jami'an tsaron Burkina Faso a birnin Ouagadougou, ranar 27 ga watan Nuwamba, 2021. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Dandazon Jama'ar dai sun so su gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gazawar shugaba Roch Marc Christian Kabore kan dakile tashe-tashen hankulan da 'yan ta’adda masu ikirarin jihadi ke haddasawa da suka dabaibaye sassan kasar, amma kuma hukumomin tsaron suka dakile gangamin.

Gamayyar kungiyoyin fararen hula uku ne suka shirya jagorantar zanga-zangar lumanar ta ranar Asabar din 27 ga watan Nuwamba, don yin tir da karuwar rashin tsaro tare da neman shugaba Kabore ya yi murabus.

Sai dai duk da dakile zanga-zangar, sai da WASU fusatattun matasa suka kafa shingayen wucin gadi tare da kona tayoyi a unguwanni da dama a birnin Ouagadugou, ciki har da yankin harabar hedkwatar jam’iyya mai mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.