Isa ga babban shafi
China - Afirka

Senegal ta nemi taimakon China kan warware matsalolin Yankin Sahel

Gwamnatin Senegal ta bukaci China ta sanya hannu wajen shawo kan matsalolin tsaro tashin hankalin da suka addabi Yankin Sahel.

Ministar harkokin wajen Senegal Aissata Tall Sall.
Ministar harkokin wajen Senegal Aissata Tall Sall. © Wikipedia
Talla

Ministar harkokin wajen kasar Aissata Tall Sall ta bayyana haka ne bayan ganawa da takwaranta na China Wang Yi, inda ta bayyana fatan ta na ganin Chinar ta daga muryar ta wajen yaki da yan ta’adda a Yankin.

Ganawar ministocin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fara taron China da kasashen Afirka a Senegal.

Ana sa ran shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi, da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da kuma shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa za su halarci taron na Senegal.

Kasar Sin dai tana zuba jari sosai a Afirka, abinda ya sanya ta zama babbar abokiyar ciniki a nahiyar, inda kididdiga ta nuna cewar, an samu ciniki kai tsaye tsakaninta da kasashen nahiyar ta Afirka da darajarsa ta kai dalar Amurka biliyan 200 a shekarar 2019, kamar yadda ofishin jakadancin kasar ta Sin dake Dakar ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.