Isa ga babban shafi
RIKICIN-MALI

ECOWAS ta yi barazanar kara wa Mali takunkumai

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS sun sake jaddada bukatar su ta ganin shugabannin sojin Malin sun gudanar da zaben shugaban kasa a watan Afrilu ko kuma aka sanya musu sabbin takunkumin karya tattalin arziki a watan Janairu.

Shugaban ECOWAS Nana Akufo-Addo da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen taron kungiyar
Shugaban ECOWAS Nana Akufo-Addo da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wajen taron kungiyar © Nigeria presidency
Talla

Bayan taron da shugabannin da suka gudanar a Najeriya, shugaban gudanarwar kungiyar Jean-Claude Brou yace shugabannin sun jaddada matsayin su na ganin an gudanar da zaben shugaban kasar Mali a ranar 27 ga watan Afrilu kamar yadda aka shirya a baya.

Shugaban sojin Mali Kanar Assimi Goita ya sanar da cewar a karshen watan Janairu mai zuwa zai shaidawa kungiyar ECOWAS shirin sa na gudanar da zabe mai zuwa.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed wajen taron ECOWAS
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed wajen taron ECOWAS © Nigeria presidency

Ita dai kungiyar ECOWAS ta dakatar da Mali daga cikin ta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi sau biyu a watan Agustan shekarar 2020 da watan Mayun shekarar 2021 tare da kakabawa shugabannin sojin haramcin tafiye tafiye da kuma rufe asusun ajiyar su.

Shugaban sojin Malin yace dalilin dage zaben watan Fabarairun ya biyo bayan taron kasa da ya kaddamar domin baiwa jama’a damar bayyana ra’ayoyin su akan yadda za’a samar da zaman lafiya a kasar.

Wasu daga cikin shugabannin ECOWAS dake halartar taron kungiyar  a Abuja
Wasu daga cikin shugabannin ECOWAS dake halartar taron kungiyar a Abuja © Nigeria presidency

Goita ya zama shugaban mulkin sojin Mali bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara.

Rahotanni sun ce kungiyoyin fararen hula da dama sun kauracewa taron ‘yan kasa da gwamnatin sojin Mali ta fara gudanarwa ayau lahadi.

Kasar Mali ta fada tashin hankali tun bayan kifar da gwamnatin farar hular kasar shekaru 6 da suka gabata, abinda ya haifar da kungiyoyin ‘Yan ta’adda dake dauke da makamai wadanda ke neman iko a sassa daban daban na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.