Kananan hukumomi 538 ke da tsaro a Mali daga cikin 749 dake kasar
Rahotanni daga kasar Mali na nuna cewar akalla kananan hukumomi 538 ke da cikakken tsaro daga cikin 749 da ake da su, samakamon matsalolin 'Yan bindigar da suka addabi kasar.
Wallafawa ranar:
Wannan ya fito fili ne lokacin fara wani taron al'umma da akayi jiya asabar wanda ake saran yayi nazari akan matsalolin tsaron da suka addabi kasar tun bayan juyin mulkin farko da akayi.
Ana sa ran nan da ranar 30 ga wannan wata na Disamba, wakilan jama’a dake halartar wadanan tarurruka za su gabatar da shawarwari na gari da za su taimaka wajen shimfda sabon babi dangane da tafiyar da mulkin kasar daga matakin kananan hukumomi zuwa na shugaban kasa.
Majalisar sojin kasar ta Mali ta tsaya kan bakar ta na cewa ya zama wajibi a saurari koken mutanen kasar kafin a je zabuka masu zuwa, yayin da kasashen Duniya ke ci gaba da matsin lamba akan su wajen ganin an gudanar da zabe tare da mika mulki ga fararren hula.
Shugaban mulkin sojin Assimi Goita yaki amincewa da bukatar kungiyar ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya na shirya zaben shugaban kasa a cikin lokacin da suke bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu