Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Faransa za ta janye dubban dakarunta daga Sahel

Faransa za ta rage dakarunta a yankin Sahel zuwa dubu 3  sabanin dubu 5, nan da wasu 'yan makwanni, a karkashin babban  garanbawul din da take yi wa rundunar sojojinta a yankin kamar yadda babban Kwamandan Rundunar Yaki da 'Yan ta’adda ta Barkhane, Janar Laurent Michon ya sanar da AFP.

Wasu daga cikin sojojin Barkhane a Mali
Wasu daga cikin sojojin Barkhane a Mali © RFI Mandenkan / Sory Ibrahim
Talla

A game da burin da ake da shi na son sake fasalta rundunar sojin Faransar a yankin Sahel a 2022 mai shirin kamawa, Babban Kwamandan Rundunar ta Bakhan ya bayyana cewa,  suna kan mataki na karshe ne, abin nufi shi ne na janye sojojin da ke  yankin arewacin kasar Mali a garuruwan Tombouctou, Kidal, da Tessalit), a wani sa’in aikin na tafiya ne tare da sa hannun mahukuntan Mali, da kuma na rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma, sai kuma aminai na rundunar hadin guiwar kasashe, wato  Takuba.

Janye dakarun da ke tafiya mataki-mataki na tafiya dai dai kamar yadda ake bukata.

A wannan fage da aka raba tsakanin rundunar Faransa da ta dakarun Majalisar Dinkin Duniya Minusma, alakar za ta ci gaba da tafiya ne ba canji domin dakarun Mali ne za su canji sojin na Faransa a cewar kwamandanna Barkhan

Zango na biyu na janye dakarun kuma, zai fara a cikin watanni 3 masu zuwa

Yanzu haka dai a wannan shekara ta 2021 dakarun Faransa dubu 5 ne a yankin Sahel a yayin da za su zama dubu 300 a shekara ta 2022 mai shirin kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.