Isa ga babban shafi
Mali

Mali na taron kasa kan mayar da mulki hannun farar hula

Gwamnatin Mali da ke karkashin mulkin soja ta kaddamar da taron kasa na kwanaki hudu, kan shirin maida da kasar zuwa mulkin farar hula, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan shekarar 2020.

Assimi Goita, shugaban sojin rikon kwaryar Mali.
Assimi Goita, shugaban sojin rikon kwaryar Mali. AFP - ANNIE RISEMBERG
Talla

Yayin kaddamar da bude taron a ranar Litinin da ta gabata, shugaban rikon kwaryar Mali Kanal Assimi Goita, ya ce taron na kasa dama ce ga jama'a don samar da sauyi, ta hanyar gabatar da shawarwarin samar da mafita don kawo karshen matsalolin da kasar ke fama da su.

Sai dai tuni manyan kungiyoyin masu fafutuka da kuma ‘yan adawa suka caccaki taron, tare da shan alwashin kaurace wa halartarsa.

Tarihi dai ya nuna cewar kasar Mali ba ta samun dadewa a karkashin mulkin farar hula tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekara ta 1960.

A watan Agustan shekarar 2020, sojoji a karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita suka hambarar da zababben shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita, bayan zanga-zangar da ya fuskanta tsawon makwanni saboda zargin sa da cin hanci da kuma gaza kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi.

Bayan fuskantar matsain lamba daga Faransa da makwafta ne kuma, Kanal Goita ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a watan Fabrairun shekarar 2022 bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Amma a watan Mayun bana, Kanal din ya sake jagorantar juyin mulki na biyu, abin da ya kawo karshen gwamnatin farar hula ta wucin gadi, ya kuma haifar da cikas ga jadawalin gudanar da sabon zabe.

Sai dai a ranar 12 ga watan Disamba, Goita ya shaida wa kungiyar ECOWAS cewa, zai gabatar da sabon jadawalin zabe nan da ranar 31 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.