Isa ga babban shafi
Nijar-Rwanda

Nijar ta kori mutanen da suka yi kisa a Rwanda

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun kori ‘yan asalin kasar Rwanda su 8 da aka zarga da hannu a  kisan kiyashin kasar na shekarar 1994 bayan share tsawon makonni da isarsu  birnin Yamai.

Kimanin mutane dubu 800 suka rasa rayukansu a lokacin rikicin Rwanda a shekarar 1994
Kimanin mutane dubu 800 suka rasa rayukansu a lokacin rikicin Rwanda a shekarar 1994 Thomson Reuters Foundation / Nit
Talla

Wata sanarwa da Ministan Cikin Gidan Jamhuriyar Nijar Hamadou Amadou Souley ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an bai wa mutanen 8 umurnin ficewa daga kasar saboda dalilai na diflomasiyya, lura da cewa yanzu haka mutanen na cikin jerin wadanda kotun duniya ta musamman da aka kafa don hukunta masu hannu a rikicin Rwanda ke nema ruwa a jallo.

Tuni kungiyar agaza wa mutanen da rikicin Rwanda ya rutsa da su, ta yi lale marhabin da matakin da Nijar ta dauka, tana mai cewa, hakan tamkar izina ce ga sauran masu hannu a kisan kare dangin wadanda kuma ake nema domin hukunta su.

Daga cikin mutanen takwas da aka kora,  Kotun ta Majalisar Dinkin Duniya, ta samu hudu da aikata manyan laifuka da suka hada da tsohon kwamandan sojojin Rwanda, Alphonse Nteziryayo da tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin kasar, Antole Nsengiyumva da kuma wasu tsaffin sojoji guda biyu.

Bayanai na cewa, gwamnatin Nijar ta kori wadannan mutane ne bayan takwararta ta Rwanda ta nuna fushinta karara kan yadda aka ba su mafaka a Yamai kamar yadda jaridar Jeune Afrique ta rawaito.

Sanarwar da Ministan Cikin Gidan Nijar din ya fitar, ta ce, daga yanzu, an haramta wa mutanen zama na din-din-din a kasar saboda dalilai na diflomasiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.