Isa ga babban shafi

Shugaban hukumar CAF zai halarci gasar Afrika a Kamaru

Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika dan Afrika ta Kudu Patrick Motsepe tareda rakiyar matar sa ya sauka kasar ta Kamaru.

Shugaban hukumar CAF Patrice Motsepe
Shugaban hukumar CAF Patrice Motsepe Phill Magakoe AFP/Archives
Talla

Shugaban na Caf ya ce ba gudu ba ja da baya, zai kasance  a kasar ta Kamaru  a lokacin bikin bude gasar cin kofin kwallon kafar Afrika tareda rakiyar mai dakin sa duk da kashedin da wasu ke yi na cewa cutar Covid 19 na barrazana ga lafiyar mahalarta wannan ganggami.Motsepe ya ce kasancewa wasu kasashen sun samu nasara wajen shirya tarurruka a baya, to mai zai hana kungiyar CAF cimma haka,da saukar sa ya na mai cewa ga ni na zo ganewa idanun na irin wainar da za a tuya  kasar ta Kamaru.

Gasar cin kofin Afrika ma Kamaru
Gasar cin kofin Afrika ma Kamaru © Courtesy of CAF

Duk da isowar Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika kasar ta Kamaru,hukumar Caf ta dau matakan da suka dace don kaucewa yaduwar kwayar cutar yayin gudanar da wannan gasa,matakan da suka hada da rage yawan yan kalo a filayen wasanni,banda haka  bukatar  ganin yan kalon da suke bukatar shiga filayen wasanni sun gabatar da sheidar dake tabbatar da cewa sun karbi allurar rigakafin cutar   sau biyo.

Samuel Eto'o Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru
Samuel Eto'o Shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru AFP/Archivos

Za a yi wannan gasa ta cin kofin Afrika kama daga ranar  9 ga wannan wata na janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun shekarar 2022 da muke ciki.

 

Ranar 9 Kamaru mai masaukin baki za ta ketse reni da  Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.