Isa ga babban shafi
Kamaru - Burkina Faso

Burkina Faso ta zargi Kamaru da shirin yi mata kwange a gasar AFCON

Takaddama ta barke tsakanin tawagar kwallon kafar kasar Burkina Faso da jami’an Kamaru, gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a kasar ta Kamaru, inda kaftin din Burkina Faso ya caccaki gwajin cutar Korona da aka yi musu.

Kofin gasar Afcon da za ta gudana a Kamaru
Kofin gasar Afcon da za ta gudana a Kamaru AFP - DANIEL BELOUMOU OLOMO
Talla

Kyaftin din mai suna Bertrand Traoré ya bayyana gwajin cutar a matsayin abin kunya a daidai lokacin da suka kammala shirye-shiryen na bude gasar AFCON da fafatawa da Kamaru yau Lahadi a filin wasa na Olembé da ke Yaoundé.

Kasashen da suka samun tikitin gasar cin kofin Afrika na kamaru
Kasashen da suka samun tikitin gasar cin kofin Afrika na kamaru Vincent LEFAI AFP

Traoré da mataimakin kocin Burkina Faso Firmin Sanou sun ce tawagar likitoci sun taru a otal dinsu da ke Yaoundé da safiyar ranar Juma'a don gudanar da gwaje-gwaje, kuma lokacin da suka nemi tabbatar da shaidarsu, Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF, ta musanta aika tawagar jami’an lafiyar.

A halin yanzu dai sakamakon gwajin da tawagar likitocin suka fitar ya nuna cewar, kocin tawagar kwallon kafar Burkina Faso Kamou Malo da 'yan wasan baya Sa’idou Simporé da Oula Abass Traoré da kuma dan wasan gaba Dango Outtara suna dauke da cutar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.