Isa ga babban shafi
Uganda

Daliban Uganda sun kammala hutun dole na shekaru 2 saboda Korona

Uganda ta kawo karshen rufe makarantun kasar, mataki mafi dadewa da aka dauka kan sha’anin ilimin a duniya, inda ta umarci miliyoyin dalibai da su koma aji bayan tazarar kusan shekaru biyu.

Wasu daliban Firamare a kasar Uganda.
Wasu daliban Firamare a kasar Uganda. Kimberly Burns, USAID/CC/Pixnio
Talla

Kimanin dalibai miliyan 15 ne ba su halarci makarantunsu a Uganda ba tun cikin watan Maris na shekarar 2020 lokacin da aka rufe ajujuwa yayin da annobar Korona ta mamaye duniya.

A Satumban bara ne dai shugaban Uganda Yoweri Museveni ya janye dokokin hana walwalar da ya kafa domin dakile yaduwar cutar ta Korona a kasar amma ya bar makarantu a rufe, inda sai a watan Oktoban shekarar ta bara ya sanar da cewa, za a sake bude makarantun ne a farkon shekara nan da muke ciki.

Tun a waccan lokacin dai, kungiyoyin kare hakkin yara suka soki matakin gwamnatin Uganda na rufe makarantu gaba daya kuma na tsawon makonni 83, wa’adi mafi tsawo a duniya.

A ranar 7 ga Janairun nan Alkaluman hukumomin lafiya suka nuna Uganda ta sami adadin mutane 153,762 da suka kamu da Korona, yayin da annobar ta kashe 3,339, tun bayan bulla a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.