Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Sojoji sun sanar da kwace mulki a Burkina Faso

Sojoji a Burkina Faso sun sanar da kwace mulki a kasar da ke yammacin Afirka, bayan boren da wani gungu daga cikinsu ya jagoranta kan yadda shugaban kasar ya kasa shawo kan matsalar hare-haren ta’addancin mayaka masu ikirarin jihadi.

Kyaftin Sidsoré Kader Ouedraogo ta kafar gidan talabijin na Burkinabè (RTB), yayin sanar da kwace mulki da sojoji suka yi a Burkina Faso. Janairu 24, 2022.
Kyaftin Sidsoré Kader Ouedraogo ta kafar gidan talabijin na Burkinabè (RTB), yayin sanar da kwace mulki da sojoji suka yi a Burkina Faso. Janairu 24, 2022. © RTB/Capture d'écran
Talla

Wani karamin jami’in soja ne ya sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, da rusa gwamnati da majalisar dokokin kasar, da kuma rufe iyakokin kasar daga tsakar daren Litinin din nan, kamar yadda sanarwa mai dauke da sa hannun Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ta fayyace.

Kyaftin Sidsoré Kader Ouedraogo, ya ce sabuwar kungiyarsu ta sojoji ‘yan kishin kasa mai suna, ‘MPSR’ a takaice,  za ta sake kafa tsarin tsarin mulki a cikin lokacin da ya dace, inda ya kara da cewa za a kafa dokar hana fitar dare a fadin kasar.

Da safiyar yau Litinin ne dai manyan kasashen Afirka da na yammacin Turai suka yi tir da abin da suka kira yunkurin juyin mulki, yayin da kuma kungiyar EU ta bukaci a gaggauta sakin shugaba Roch Marc Christian Kabore da sojoji suka kama.

Amurka ta kuma yi kira da a saki Kabore tare da yin kira ga jami'an tsaro da su mutunta kundin tsarin mulkin Burkina Faso da shugabancin farar hula.

Shi ma dai Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres cikin sanarwar da ya fitar, yayi tir ne da yunkurin kwace gwamnati da karfin tsiya, matakin da ya bayyana a matsayin juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.