Guguwar Ana, ta kashe mutane sama da 70 a Mozambique, Malawi da Madagascar.
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar Ana, da ta haddasa ambaliyar ruwa a kasashen Mozambique, Malawi da Madagascar sun kai 70.A cewar hukumomin kasashen, adadin ka iya karuwa kasancewar har yanzu ana ci gaba da aikin ceto da nufin gano wasu karin mutanen.
Wallafawa ranar:
Hukumomi da masu aikin ceto na cigaba da kokarin gano musababin faruwar hakan a kasashen uku da kuma taimaka wa wanda suka jikata.
Wannan dai na zuwa ne bayan da makeken kogi ya yi awon gaba da wasu jami’ai da gwamnatin kasar ta aika don tattaron bayani a game da bannar da guguwar da kuma ambaliyar ruwan suka haddasa.
A rahoton da Madagaskar ta fitar ta ce mutane 41 sun cimma ajalinsu a yayin da 18 suka mutu a Mozambik, sai guda 11 da suka rasa rayukan su a kasar Malawi.
Lamarin a Madagaskar ya sanya daruruwan mutane barin gidajensu, abinda ya sanya makarantu da wuraren motsa jiki suka zama sansanin gudun hijira.
Ko a Mozambique ma haka lamarin yake, don kuwa tuni gwamnatin kasar ta ce, a yanzu tana mayar da hankali ne wajen gyara turakun wutar lantarki da guguwar ta lalata, da nufin baiwa asibitoci lantarki don kulawa da marasa lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu