Isa ga babban shafi
Faransa - Burkina Faso

Sojin Faransa ta sanar da kashe 'yan ta'adda kusan 60 a Burkina Faso

Rundunar Sojin Faransa tace dakarun Burkina Faso da taimakon su sun kashe ‘Yan ta’adda kusan 60 a wata arangamar da suka yi a yankin.

Wani sojin Burkina Faso na tattaki kusa moitar sojojin Faransa
Wani sojin Burkina Faso na tattaki kusa moitar sojojin Faransa © (AP Photo/Sam Mednick)
Talla

Sanarwar da rundunar sojin ta gabatar ta nuna cewar sau 4, wato tsakanin ranakun 16 ga watan Janairu zuwa 23 suka gano da kuma hallaka ‘Yan ta’adda a maboyar su sakamakon hadin gwuiwa tsakanin dakarun Burkina Faso da na Faransa.

Kasar Burkina Faso na fuskantar barazanar ‘Yan ta’adda tun daga shekarar 2015 lokacin da mayakan dake da alaka da kungiyar Al Qaeda da IS suka fara tsallaka iyaka daga Mali suna kai musu hari.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace mutane sama da 2,000 suka yi asarar rayukan su sakamakon irin wadannan hare hare a cikin kasar.

Hukumar agajin gaggawa a Burkina tace mutane sama da miliyan guda da rabi suka rasa matsugunin su sakamakon tashin hankalin, kuma kashi biyu bisa uku daga cikin su yara ne kanana.

A ranar 14 ga watan Nuwambar bara, wata tawagar ‘Yan ta’adda dauke da daruruwan mutane ta kai hari Inata dake iyakar Mali inda ta kashe mutane 57, cikin su harda jandarmomi 53.

A ranar 23 ga watan Disamba, mutane 41 aka kashe lokacin da ‘Yan ta’addan suka kai hari akan tawagar Yan kasuwa kusa da Ouahigouya kusa da iyakar Malin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.