Isa ga babban shafi
MALI-ECOWAS-ALJERIA

Aljeriya na kokarin sasanta kasar Mali da kungiyar ECOWAS/CEDEAO

Ministan harakokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra, ya bayyana aniyar kasarsa na son shiga tsakanin sasanta kasar Mali da kungiyar Ecowas ko Cedeao, inda ya ce babu wani amfani ga rishin jituwarsu, illa baiwa kungiyoyin yan ta’adda damar ci gaba da shirya kai hare- harensu na ta’addanci.

Ministan wajen kasar Aljeriya Ramtane Lamamra à Addis-Abeba le 4 février 2022.
Ministan wajen kasar Aljeriya Ramtane Lamamra à Addis-Abeba le 4 février 2022. © F24/RFI
Talla

A tattaunawar da ta hada shi da kafofin Radiyo  da Talabijin na RFI da France 24, Ramtane Lamamra ya yi fatan ganin cewa,  har yanzu da sauran  lokaci da ya kamata kasashen duniya su yi amfani da shi wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyansu, wajen magance matsalar.

Don haka a cewarsa Aljeriya a shirye take shirya tattaunawar shiga tsakani buda tattaunawar yan uwantaka tsakanin Mali da sauran makwaftanta na kungiyar  Ecowas ko  Cédéao.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.