Isa ga babban shafi
Tarayyar Afirka

Taron AU na 35th zai tattauna matsalar yawaitar juyin mulki a Afirka

Shugabannin kasashen Afrika sun fara wani taro na kwanaki 2 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, wanda shine karon farko da suke tozali da juna tun bayan bullar annobar Covid 19 a shekarar 2019.

Shugabannin kasashen Afirka da wakilai na taro karo na 35th a Adis Ababa na Habasha.
Shugabannin kasashen Afirka da wakilai na taro karo na 35th a Adis Ababa na Habasha. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Taken taron nasu na wannan karon shine ‘Gina jajircewa a kan abinci mai gina jiki a nahiyar Afrika’, sai dai akwai batutuwa da dama da suka  zame wa shugabannin wajibi su nazarta.

Ko a jiya Asabar da aka fara taron karo na 35th, shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya yi bitar dabaru da shirye shiryen nahiyar wajen yaki da annobar Covid-19.

Shugabannin na Afrika za su kuma tattauna batun matsalar juyin mulki da soji ke yi a nahiyar, musamman yankin yammaci, biyo bayan hambarar da gwamnatoci aq Burkina Faso, Mali, Guinea da Soudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.