Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Firaminista Maiga ya zargi Faransa da yunkurin raba Mali gida biyu

Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga ya zargi kasar Faransa da neman raba kasar gida biyu lokacin da ta jagoranci sojojin ta wajen aikin yakin da ‘Yan ta’adda a cikin kasar.

Firaminista Choguel Maïga na Mali.
Firaminista Choguel Maïga na Mali. AFP - KENA BETANCUR
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito Firaministan na shaidawa jami’an diflomasiyar kasashen waje wannan matsayi a ci gaba da takun sakar da ake samu tsakanin Mali da Faransa.

Maiga yace tabbas kai sojojin Faransa Mali a shekarar 2013 ya taimaka wajen rage ayyukan masu ikrarin jihadi da suka kama wani yanki na arewacin kasar da kuma yiwa yankin kudanci barazana.

Sai dai yayi zargin ayyukan sojojin Faransa ya koma na raba kasa daga baya, wajen baiwa ‘Yan ta’addan damar sake taruwa a cikin kasar da kuma kaddamar da hare hare a shekarar 2014.

Firaministan ya kawo misali akan yadda Faransa suka bukaci Amurka ta janye dakarun ta daga kasar su bayan yakin duniya na biyu saboda basa bukatar su, amma kuma Amurkawan basu mayar da martani wajen zagin Faransawan ba.

Tuni dai Faransa ta bayyana cewar tana nazari dangane da ci gaba da zaman sojojin ta a Mali bayan da gwamnati ta kori Jakadan ta a makon jiya.

Takaddama ta kara kaimi tsakanin kasashen biyu bayan da shugaba Emmanuel Macron ya cacaki sojojin dake mulkin kasar da gazawa wajen kin mutunta shirin mayar da mulki hannun fararen hula.

Kasar Mali ta kara kaimi wajen sukar Faransa bayan da ECOWAS ta sanya mata takunkumi a ranar 9 ga watan Janairu, abinda ya sa Mali ke zargin Faransa da hannu wajen daukar matakin.

Maiga ya ce ba za su bari a ci gaba da musu mulkin mallaka ba, domin lokacin yin haka ya wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.