Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

Sojin Faransa sun kashe mayaka masu ikirarin jihadi 30 a Mali

Akalla mayaka masu ikirarin jihadi 30 ne aka kashe, tare da lalata gwamman ababen hawa da makamansu, a wasu hare haren hadin gwiwa da dakaru na musamman, karkashin jagorancin Faransa da sojojin Mali suka kai sansanoninsu, kamar yadda ma’aikatar kula da ayyukan sojin Faransa ta sanar.

Sojin Faransa da ke yaki da ayyukan ta'addanci a arewacin Mali.
Sojin Faransa da ke yaki da ayyukan ta'addanci a arewacin Mali. Thomas COEX AFP/File
Talla

Ma’aikatar kula da ayyukan sojin Faransa tace a yayion samamen da dakarun hadin gwiwar suke yi ne jirage marasa matuka suka hango ‘yan ta’addan  bisa babura, kuma ba su yi wata-wata ba, suka aika musu da jiragen yaki, kirar Mirage 2000 don taimaka wa dakarun da suka yi musu dirar mikiya ta kasa.

Sanarwar ta kara da cewa gwamman kilogram na abubuwa masu fashewa, makamai da babura, wadanda ‘yan ta’addan ke amfani da su ne aka lalata a samamen.

Hare haren hadin gwiwar na ranar 1 zuwa 6 ga watan Fabrairun nan sun zo ne a lokacin da dangantaka tsakanin Faransa da Mali ke dada tsami, lamarin da ya tilasta wa Faransar da sauran abokanta na Turai diga ayar tambaya a kan ci gaba da zaman dakarunsu a Mali.

Kawayen Faransa na Turai sun shirya tsaf don yanke shawara a kan yadda za su ci gaba da yakin kawar da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a Mali, su na mai bayyana halin da ake ciki a matsayin  mai wuyar sha’ani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.