Isa ga babban shafi
Amurka - Kamaru

Amurka da Kamaru sun 'keta' 'yancin masu neman mafaka: HRW

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Kamaru da na Amurka da aikata “take hakkin dan adam" mafi muni kan 'yan kasar da dama da Amurka ta mayar da su kasar da ke yankin tsakiyar Afirka.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, 10 ga watan Oktobar 2019.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, 10 ga watan Oktobar 2019. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Cikin wani rahoto mai shafuka 174 da Human Right Watch ta fitar ta zargi Amurka da taimakawa Kamaru wajen maido da ‘yan kasar kimanin 80-90 zuwa gida cikin jirage biyu a watan Oktoba da Nuwambar shekarar 2020.

Inda suka fuskanci tsarewa ba bisa ka’ida ba; bacewar wasu; azabtarwa da fyade, da kuma sauran tashin hankali, ko kuma karban cin hanci.

Yankin 'Yan aware

Kusan dukkanin wadanda Amurkan ta dawo da su gida Kamaru, sun fito ne daga yankin tsirarun masu amfani da turancin Ingilishi a yammacin kasar, inda mayakan 'yan awaren dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia ke fafatawa da sojojin gwamnati da suka shafe shekaru biyar cikin kazamin rikici, inda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu ke zargin bangarorin biyu da cin zarafin jama'a.

Rahotan yace "da yawa daga cikin mutanen sun fuskanci cin zarafi da suka hada da amfani da  karfi fiye da kima, rashin kulawar likita, da sauran cin zarafi a hannun hukumomin Shige da Fice da Hukumar Kwastam na Amurka.

Amurka ta keta 'yancin mafaka

Kungiyar tace da wannan mataki da Amurka ta dauko na maido da ‘yan kasar Kamaru gida duk da ta kwana da sanin barazanar zalunci da suke fuskantar da  azabtarwa, to lallai ta keta 'yan mafaka da na kare hakkin bil'adama."

Gwmanatin Trump

Rahoton ya ce an kori mutanen ne a karkashin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, "wanda ke da tsattsauran ra'ayi na shige da fice, da takaita samun mafaka, da kalaman wariyar launin fata,"

Gwamantin Biden

HRW tace, yayin da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta "dauki kyakkyawar matakin soke wani jirgin ‘yan kasar Kamaru zuwa gida a watan Fabrairun shekarar 2021, amma abin takaici ta kori 'yan kasar da dama cikin watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.