Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Faransa na fuskantar turjiya a kasashen Afrika

Karbuwar Faransa a kasashen da ta yi musu mulkin mallaka a Afrika na ci gaba da sukurkucewa duk da cewa, sojojinta sun kwashe tsawon gomman shekaru suna yaki da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Wasu daga cikin sojojin Faransa masu fada da kungiyoyin jihadi a Sahel.
Wasu daga cikin sojojin Faransa masu fada da kungiyoyin jihadi a Sahel. AP - Jerome Delay
Talla

Tun bayan da ta kawo karshen mulkin mallakanta a kasashen Afrika a tsakan-kanin shekarun 1960 a Afrika, har yanzu Faransa na ci gaba da shan zarge-zargen mamaye ayyukan soji da kuma tattalin arzikin kasashen na yankn Sahel, inda take mara baya ga shugabannin da ke biyayya a gare ta.

Duk da cewa, Faransar ta hakikance cewa, ba ta da niyar mamaye ikon kasashen yammacin Afrika, amma tana ci gaba da shan suka a yankin musamman saboda yadda ta gaza kakkabe kungiyoyin mayakan jihadi da suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu a cikin shekaru 10 da suka shude.

Kyamar da ake nuna wa Faransar ta ma fi kamari a kasar Mali musamman bayan da sojojin da ke mulki a kasar suka fitar da wasu sakwanni da suka kara tunzura jama’a.

Masharhanta sun ce, dakarun Barkhane karkashin jagorancin Faransa da ke kokarin kakkabe ‘yan ta’adda a Sahel, ana kallon su a matsayin wani yunkuri na Faransa domin ci gaba da tsoma baki cikn lamurran cikin-gidan kasashen na Afrika.

Tun shekara ta 2013, Faransa ta fara tsoma baki a rikicn Mali bayan gwamnatin kasar ta waccan lokacin ta gayyace ta.

Sai dai har yanzu ba ta kammala kakkabe daukacin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar ba, hasali ma sun kara karfi ne tare da yaduwa zuwa kasashe makwabta irinsu Nijar da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.