Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Damiba ya sha rantsuwar shugabancin Burkina Faso

An rantsar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a matsayin sabon shugaban Burkina Faso, bayan wasu ‘yan makwanni da ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore.

Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba,
Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba, via REUTERS - Burkina Faso Presidency Press Se
Talla

A wani biki da aka watsa ta kafar talabijin, Damiba ya sha rantsuwar kama aiki a gaban babban kwamitin fasalta kundin tsarin mulkin Burkina Faso, inda ya yi alkwarin karewa da kuma mutunta dokokin kundin tsarin mulkin kasar.

Damiba dai ya sanya kakin soji tare da kifa wata jar-hula, sannan ya yafa wani gwado mai dauke da launin tutar kasar ta Burkina Faso.

An dai bai wa kafafen yada labarai damar halartar bikin rantsuwar domin daukar rahoto, amma babu wani bako daga ketare da ya halarci bikin wanda aka gudanar a wani karamin daki da ke ofishin kwamtin fasalta kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar 24 ga watan  Janairu ne, Damiba mai shekaru 41 ya jagoranci wasu fusatattun sojoji har suka kawar da  shugaba Kabore daga kujerarsa bayan al’ummar kasar sun yi ta korafi kan sakacinsa wajen yaki da masu ikirarin jihadi a kasar.

Burkina Faso dai na cikin kasashe mafiya fama da takauci a duniya, kuma tana cikin masu fama da ayyukan ta’addanci a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.