Isa ga babban shafi
Kamaru

An sace jami'an kungiyar likitocin kasa da kasa 5 a Kamaru

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ma'aikata biyar na kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF a Arewa mai Nisa da ke kasar Kamaru, yankin da ke fama da matsalar 'yan tada kayar baya.

Wani yankin a Arewa mai nisa na kasar Kamaru.
Wani yankin a Arewa mai nisa na kasar Kamaru. AFP - PATRICK MEINHARDT
Talla

Kungiyar likitocin da kuma wani babban jami'in yankin na Arewa mai Nisa a Kamarun sun lamarin ya auku ne a Alhamis da ta gabata, inda wasu mutane dauke da makamai a Fotokol, kusa da kan iyaka da Najeriya, a suka shiga wani gini da MSF ke amfani da shi, suka kuma sace jami’ai 5.

Mutanen da aka yi garkuwa da su, sun hada da ma'aikatan agaji uku da suka fito daga kasashen Chadi, Senegal da Ivory Coast, da kuma jami'an tsaron Kamaru biyu.

Yankin Arewa mai nisa a Kamaru da ke fama da matsalolin tsaro ya yi iyaka da Najeriya daga bangaren yammacinsa, yayin da kuma daga bangaren gabashi yayi iyaka da kasar Chadi, wadanda su ma suke fafutukar murkushe hare-haren 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.