Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Benin ta gabatarwa yan kasar da kayayyakin tarihin guda 26

Watanni uku bayan dawowa Jamhuriyar Benin da kayayyakin tarihi da Turawan mulkin mallakan Faransa suka yi awon gaba da su da sunan ganimar yaki a wancan zamani, hukumomin Jamhuriyar Benin sun gabatarwa yan kasar da wadannan kayayyakin tarihin guda 26 yayin wani bikin baje kollin kayan tarihin da ya gudana a fadar Shugaban kasar dake birnin Kwatano.

Karagar Sarkin Abomey
Karagar Sarkin Abomey AFP - CHRISTOPHE ARCHAMBAULT
Talla

Tarihi ya nuna cewa an yi awon gaba da wadannan kayayyaki ne a shekarar ta 1892, lokacin da turawan mulkin mallakar Faransa suka kwashe illahirin kayayyakin dake cikin fadar Sarkin Abomey, garin dake a matsayin babban birnin masarautar Dahomey.

Mutumutumin Sarki Béhanzin a garin Abomey
Mutumutumin Sarki Béhanzin a garin Abomey © RFI/Pierre Firtion

Yau shekaru 129 da sace wadanan  kayayyakin tarihi, kafin aka sake dawo da su gida, inda gwamnati a karkashin shugabancin Patrice Talon, wanda ya halarci bikin da ya gudana fadar sa ranar asabar 16 ga watan Fabrairun 2022 cikin farin ciki ya bayyana cewa wannan rana tamkar nasara ce ga kasar, musaman ga fanni da ya shafi al’adu, kasancewa a yau daukacin yan kasar na ganewa idanun su nasarar da gwamnati ta yi na dawo da wadanan kayayyakin tarihi a gida.

Yan kasar da baki yan yawon bude ido sun more, inda aka basu damar kai ziyara a zauren da aka baje wadanan kayayyakin tarihi a fadar Shugaban kasar dake unguwar Marina a Kwatano daga wannan wata na Fabarairu har zuwa ranar 22 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2022.

Abokin aikin mu Abdoulaye Issa da ya samu halartar bikin baje kolin wadannan kayayyaki ya gamu da baki da kuma yan kasar da dama wadanda suka je domin ganewa idan su wadannan kayayyaki da akayi nasarar mayar da su Jamhuriyar Benin.

Da dama wadanda suka zanta da shi sun bayyana farin cikin su da wannan mataki da shugaba Emmanuel Macron ya dauka na mikawa shugaba Talon wadannan kayayyakin tarihi domin mayar da su kasar.

Jamhuriyar Benin na daya daga cikin kasashe masu dinbim tarihin al’adu musamman a masarautar Abomey.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.