Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Rikicin kabilanci ya kashe mutane 440 a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kabilu masu fada da juna a Sudan ta Kudu ya kashe fararen hula 440 cikin watanni hudun shekarar da ta gabata ta 2021.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu. REUTERS - JOK SOLOMUN
Talla

Rahoton da hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a yau talata na nuna cewa rikicin da ya faru tsakanin wasu kabilu da ke rikici da juna a yankin Tambura cikin watan Yuni zuwa Satumba ne ya hallaka daruruwan fararen hular.

Rahoton majalisar ya dora alhakin rasa rayukan fararen hular kan mayakan da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da bangaren da ke adawa da su daga kabilar mataimakinsa Riek Machar ne suka afkawa juna da taimakon daidaikun mayakan da suka assasa a yankin.

Rahoton Majalisar ya ce baya ga fararen hula 440 da suka mutu a rikicin akwai kuma wasu mutum 18 da suka jikkata kana wasu mutum 74 da aka yi garkuwa da su a tsakanin lokacin na watanni 4.

Rahoton ya bayyana cewa a tsawon lokaci mata 64 sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata ciki har da yarinya ‘yar shekaru 13 wadda dandazon maza suka yiwa fyade har ta rasa ranta.

Bugu da kari, rahoton ya ce har zuwa yanzu ana laluben wasu mutum 56 da suka yi batan dabo kari kan mutum dubu 80 wadanda rikicin ya tilasta musu barin muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.