Isa ga babban shafi
Tunisia

Jami'an tsaron Tunsia sun dakile yunkurin kai harin ta'addanci

Ma'aikatar cikin gidan Tunusia ta ce jami'an tsaron kasar sun dakile wani shirin kai harin ta'addanci tare da cafke wata mata mai ikirarin jihadi da ake zargi da hannu a mummunan shirin.

Wasu jami'an 'yan sandan kasar Tunisia a birnin Tunis.
Wasu jami'an 'yan sandan kasar Tunisia a birnin Tunis. © REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce masu bincike sun yi imanin matar ta shirya yin garkuwa da 'ya'yan wasu jami'an tsaro da sojoji ne domin kokarin ganin an sako mutanen da aka samu da laifin ta'addanci.

Ana kuma zarginta da shirin kai hari kan wata cibiyar tsaro ta hanyar amfani da wata damarar bam.

Tun a shekara ta 2015 kasar Tunisia da ke arewacin Afirka ke cikin dokar ta baci, bayan wani hari da aka kashe wasu masu gadin fadar shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.