Isa ga babban shafi
Mali

Human Rights ta zargi sojojin Mali da kashe fararen hula da dama

Kungiyar Human Right Watch ta ce, sojojin Mali sun kashe akalla fararen hula 71 tun daga farkon watan Disamba zuwa yau da sunan yaki da ‘yan ta’adda da ke addabar kasar.

Wasu sojojin kasar Mali.
Wasu sojojin kasar Mali. AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Sai dai tuni gwamnatin mulkin sojin Mali ta musanta wadannan alkaluma da kungiyar ta fitar a cikin wani sabon rahotonta.

Kungiyar ta Human Rights ta ce an kashe yawancin mutanen ne ba tare da basu damar kare kansu daga tuhumar da ake musu ba, kuma ta tattara bayananta ne daga  shaidar mutane 49.

An dai shafe tsawon lokaci hukumomin kare hakkin dan na zargin sojojin Mali da cin zarafin mutane yayin yaki da ‘yan ta’adda.

Amma gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojin Mali  da ta kafu bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a shekarar 2020, a cigaba da yin watsi da irin zarge-zargen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.