Harin 'yan tawaye ya yi sanadin mutuwar mutane 12 a Congo
Akalla fararen hula 11 galibi tsoffi da kuma soji guda aka kashe sakamakon wani harin da 'yan tawaye suka kai a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wallafawa ranar:
Wani jami'in yankin Gedeon Dino ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, "yan ta'addar CODECO sun kai hari kauyen Tshotsho da daren Laraba zuwa safiyar Alhamis, inda suka kashe fararen hula 11 da adduna da bindigu – ciki harda mata da tsoffi.
Kauyen Tshotsho yana da nisan kilomita 30 ne daga ainihin lardin Ituri na garin Bunia.
Kungiyar Codeco dai wata shu’umar kungiyar kabila ce ta masu dauke da makamai da ke ikirarin kare muradan ‘yan kabilar Lendu.
kabilun Lendu da Hema sun dade suna kai ruwa rana da juna, lamarin da ya kai da sarar rayuka. tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003 kafin dakarun kiyaye zaman lafiya na Turai su shiga tsakani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu