Isa ga babban shafi
Mali

Amurka na sanya ido kan kisan da ake yi a Mali

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce tana bibiyar labarin kashe-kashen da aka yi a tsakiyar Mali, bayan da sojojin kasar da ke yankin Sahel suka ce sun kashe 'yan ta'adda sama da 200.

Wasu sojin Mali masu fada da 'yan ta'adda
Wasu sojin Mali masu fada da 'yan ta'adda AFP - MAIMOUNA MORO
Talla

A makon jiya ne rundunar sojin kasar ta Mali ta ce a tsakanin ranakun 21-31 ga watan Maris din da ya wuce ta kashe mayakan jihadi 203 a wani samame da ta kai a yankin Moura da ke tsakiyar kasar mai fama da matsalar masu jihadi.

Sai dai sanarwar ta biyo bayan rahotannin kafafen sada zumunta da ke cewa an kashe fararen hula da dama a Moura.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya kasa tantance adadin mutanen da sojojin Mali suka yi ikirarin kashewa ko kuma rahotannin da kafofin sada zumunta na yanar gizo suka yi kan mutuwar fararen hula.

Rashin samun shiga yankunan da ke fama da rikici a Mali da kuma rashin samun majiyoyin bayanai masu zaman kansu na nufin cewa alkaluman da gwamnati da kungiyoyin masu dauke da makamai suka bayar na da wuya a iya tabbatar da su.

A ranar Lahadin da ta wuce ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana bin bayanan da ke da matukar tayar da hankali kan dimbin mutanen da aka kashe a Moura tare da mika ta'aziyyarta ga iyalan fararen hula da suka mutu.

A cikin wata sanarwa da aka fitar an bayyana cewa, rahotanni da dama sun nuna cewa sojojin kamfanin Wagner na Rasha ne suka aikata kisan, yayin da wasu bayanan ke cewa sojojin Mali ne suka kashe mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.