Isa ga babban shafi
Rwanda

Kotun Rwanda ta amince da daurin shekaru 25 kan Rusesabagina

Kotun daukaka kara a kaasr Rwanda ta amince da hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari da aka yi wa tauraron fim din Hotel Rwanda, wato Paul Rusesabagina wanda aka samu da laifin ayyukan ta’addanci bara.

Paul Rusesabagina
Paul Rusesabagina AFP/Stringer
Talla

Alkalin kotun Francois Regis Rukundakuvuga ya ki amincewa da bukatar mai gabatar da kara na kara yawan shekarun daurin da karamar kotu ta masa.

Regis ya ce, tun da Rukundakuvuga bai taba aikata wani laifi ba sai a wannan karon, kotun ba za ta amince da bukatar kara masa shekaru ba, saboda haka ta amince da hukuncin daurin shekaru 25 da aka masa bara.

Rukundakuvuga mai shekaru 67 wanda ya ki zuwa zaman kotun baki daya, yau ma ya kauracewa zuwa yanke hukuncin.

Ana danganta shi da ceto rayukan mutane sama da 1,200 lokacin kisan kiyahsin da aka yi a shekarar 1994 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 800,000 akasarinsu 'Yan Kabilar Tutsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.