Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Dan jaridar Faransa Olivier Dubois ya cika shekara 1 a hannun 'yan ta'addan Mali

A ranar 8 ga watan afrilu shekara da ta gabata ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Olivier Dubois, dan jarida bafaranshe lokacin da yake aiki a garin Gao da ke arewacin kasar Mali, abin da ke nufin cewa yau shekara daya kenan cur da ake ci gaba da yin garkuwa da shi. Abdoulakrim Ibrahim Shikal ya dauke da karin bayani.

Ana ci gaba da gangamin bukatar sakin Olivier Dubois.
Ana ci gaba da gangamin bukatar sakin Olivier Dubois. © Edmond Sadaka/RFI
Talla

Kwanaki kadan dai bayan awun gaba da shi, Olivier Dubois ya bayyana karon farko a hoton dibiyon da a cikin kungiya mai da’awar jihadi karkashin jagorancin Iyad Ag Ghali ta fitar tana cewa ita ke garkuwa da shi.

Kamar dai yadda aka saba a ranar 8 ga kowane wata, rfi na bai wa ‘yan uwan dan jaridar damar isar masa da sakon fatan alkhairi.

A yau juma’a dai an shirya gudanar da jerin gwano a garin Metz da ke gabashin Faransa don nuna goyon baya ga Olivier, yayin da za a karkafa manyan alluna dauke da hotunannsa a harabar ginin ma’aikatar magajn garin birnin Montpellier kamar dai yadda kungiyar kare ‘yan jaridu ta reporters sans frontiers ta bukaci a yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.