Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Burkina Faso 16

Sojojin Burkina Faso Akalla 12, da kuma wasu jami’an tsaron sa-kai 4 ne suka rasa rayukansu, sakamakon wani hari da ‘yan ta’adda suka kai musu, a jiya Juma’a.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso AFP/SIA KAMBOU
Talla

Bayanai sun ce an kai harin ne a kan wani karamin barikin soji mai suna Namissi-guima da ke arewacin kasar.

Arewacin Burkina Faso dai ya rikide zuwa cibiyar hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi wadanda suka fara kai hare-haren cikin kasar daga makwabciyar ta Mali a shekarar 2015.

Alkaluman baya bayan nan kuma sun nuna cewar, zuwa yanzu tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 2,000, tare da raba wasu kusan miliyan 2 da muhallansu.

Tun cikin watan Janairun da ya gabata, Burkina Faso ta kasance a karkashin mulkin soja da Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi saboda gazawar zababben shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore wajen murkushe matsalar ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.